Babu wani mahajjaci dan Najeriya da zai rasa aikin Hajjin 2025 – Shettima

Babu wani mahajjaci dan Najeriya da zai rasa aikin Hajjin 2025 – Shettima

Spread the love

Babu wani mahajjaci dan Najeriya da zai rasa aikin Hajjin 2025 – Shettima

Hajji

Daga Salisu Sani-Idris

Abuja, Feb. 10, 2025 (NAN) Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya bada tabbacin cewa babu wani mahajjaci dan Najeriya da zai rasa aikin hajjin 2025 a kasar Saudiyya.

Shettima ya bayar da wannan tabbacin ne a ranar Litinin din da ta gabata yayin wani taro da hukumar gudanarwa da hukumar alhazai ta kasa (NAHCON) da aka gudanar a ofishin sa dake fadar shugaban kasa ta Villa, Abuja.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa Shettima ya kira taron ne biyo bayan takaddamar kwangilar da ta kunno kai tsakanin NAHCON da mai bada sabis na Saudiyya, Mashariq Al-Dhahabiah, wanda ka iya janyo hana maniyyatan Najeriya biza.

Mataimakin shugaban kasar ya kuma jaddada cewa ayyukan hajjin na shekarar 2025 za su kasance cikin nasara.

Shettima ya umurci shugabannin NAHCON da su dauki dukkan matakan da suka dace don ganin an gudanar da aikin hajji cikin kwanciyar hankali ba tare da cikas ba ga dukkan maniyyatan kasar nan.

“Ba za mu bar kowane mahajjaci dan Najeriya ya rasa hajjin 2025 ba. Aikin hajjin zai kasance babu matsala kuma kowane kalubale za a magance shi cikin gaggawa,” in ji Shettima.

Shettima ya umurci shugabannin NAHCON da su dauki dukkan matakan da suka dace don kare muradun alhazan Najeriya.

“Wajibi ne hukumar NAHCON ta yi duk abin da ya kamata domin tabbatar da ganin alhazanmu za su halarci aikin ba tare da wani shamaki ba.

“Daga yanzu, dole ne mu tsara matakan da suka dace, mu bi hanya mai kyau kuma mu yi aikin Hajji ba tare da wata matsala ba.”

Dangane da batun soke kwangilar da aka yi da kamfanin da ke kasar Saudiyya, Shugaban Hukumar NAHCON, Farfesa Saleh Usman, ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa lamarin ba zai shafi aikin Hajji ba.

“Babu wani dalili na fargaba. Ba za a bar wani mahajjaci daya mai rijista ba,” in ji Usman.

Ya kuma yi watsi da zargin da Kungiyar Manyan Jami’an Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jiha, Ma’aikatu da Hukumomi ke yi cewa rikicin kwangilar na iya wargaza ayyukan Hajji na 2025.

NAN ta ruwaito cewa kungiyar ta Sakatarenta Abubakar Salihu a ranar Lahadin da ta gabata ta nuna damuwa kan soke kwangilar samar da sabis da Shugaban Hukumar NAHCON, Farfesa Saleh Usman ya yi.

Taron ya nuna fargabar cewa dubban maniyyatan Najeriya ba za su iya zuwa aikin hajjin 2025 ba saboda soke kwangilar da hukumar NAHCON ta yi.

(NAN)

SSI/ADA

Deji Abdulwahab ne ya gyara


Spread the love

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *