NAN HAUSA

Loading

Ambaliyar ruwa ta lalata gidaje, gonaki 80 a Langtang ta Kudu

 

Ambaliyar ruwa ta lalata gidaje, gonaki 80 a Langtang ta Kudu

Ambaliyar ruwa

By Polycarp Auta

Jos, Oktoba 6, 2024 (NAN) Wata mummunar ambaliyar ruwa da ta afku a karamar hukumar Langtang ta Kudu a jihar Filato, ta lalata gidaje da gonaki 80.

Ambaliyar wadda ta afku a tsakanin Juma’a da Lahadi, ta raba dubban mutane da muhallansu tare da yin awun gaba da kayayyakinsu.

Saidai an yi sa’a, ba ta yi asarar rayuka ba.

Mista Yintim Nimilam, sakataren kungiyar ci gaban al’ummar Sabon Gida, ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici, inda ya bayyana yadda sama da iyalai 80 suka rasa matsugunnansu.

“Yan gudun hijirar suna neman mafaka a gurin makwabta, abokai, da dangi,” ya ce.

Wani mazaunin garin, Mista Nandul Solomon, ya bayyana damuwar al’ummar, inda ya yi kira da gwamnati da ta dauki matakin gaggawa domin rage musu radadi.

“Muna kira ga gwamnati da hukumomin da abin ya shafa da su kawo mana dauki.” (NAN) ( www.nannews.ng )

AZA/AMM

Abiemwense Moru ne ya gyara

Fassara daga Nabilu Balarabe

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Zulum ya sake tsugunar da iyalai 424 da B’Haram ta raba da gidajensu a karamar hukumar Konduga

Zulum ya sake tsugunar da iyalai 424 da B’Haram ta raba da gidajensu a karamar hukumar Konduga

Matsugunni

By Yakubu Uba

Maiduguri, Oct. 7, 2024 (NAN) Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno ya sake tsugunar da iyalai 424 da rikicin Boko Haram ya shafa a sabbin gidaje 500 da aka gina a garin Konduga.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ya rawaito cewa mutanen da aka sake tsugunar da su sun fito ne daga garuruwan Towuri, Modu Amsamiri, Goniri, Mairamiri, Lawanti Grema Gogobe, Bula Bowuri, Zarmari, Amusari, Bula Bakaraye da kuma Furi, al’ummomin da mayakan Boko Haram suka raba da gidajensu.

NAN ta ruwaito cewa gidajen da aka tsugunar da matsugunan na da kayayyakin kamar makarantu, cibiyar kula da lafiya a matakin farko, wuraren samar da ruwa da sauran bukatu.

Da yake jawabi a wajen mika gidajen a ranar Lahadi a garin Konduga, Zulum ya lura cewa, sake tsugunar da mutanen ya nuna mafarin rufe sansanonin ‘yan gudun hijira a karamar hukumar Konduga.

Baya ga gidajen, kowane iyali ya kuma sami kayan abinci, barguna, tabarbare, katifa, bokitin roba da nannade.

Hakazalika, kowane mai gidan ya karbi Naira 50,000; yayin da matan gidan suka karbi Naira 20,000 a matsayin wani bangare na shirin sake tsugunar da su don tallafa musu wajen dibar kayan rayuwarsu.

Ya kuma jaddada aniyar gwamnatin jihar na sake tsugunar da duk wadanda rikicin tada kayar baya ya raba da muhallansu da har yanzu suna sansanoni.

“Bukatar rufe sansanonin ya zama dole a bisa yadda wasu sansanonin ke rikidewa zuwa wuraren aikata laifuka da cibiyoyin munanan dabi’u iri-iri.

“Masu aikata laifuka sun kasance suna kwana a wasu sansanonin ciki har da ‘yan Boko Haram. Wannan ba abin yarda ba ne, ”in ji Zulum.

Gwamnan ya ce gwamnatin jihar tana kuma gina gidaje 500 a unguwar Dalwa da za a kammala cikin watanni shida, a lokacin da za a sake tsugunar da su.

“Mun kuma ba da umarnin a ba da katangar Naira miliyan 100 don sake gina wasu gidaje a unguwar Aulari.”

Ya kuma gargadi wadanda suka amfana da su guji sayar da gidajen da aka ware musu.

Zulum ya bukace su da su dasa itatuwa domin yaki da hayakin Carbon da kwararowar Hamada. (NAN)YMU/SH

Edita Sadiya Hamza

Fassara daga Nabilu Balarabe

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Damfara : ‘Yansanda sun gargadi yan Nageria akan kutse a shafukkan yanar gizo

Damfara : ‘Yansanda sun gargadi yan Nageria akan kutse a shafukkan yanar gizo

Gargadi

Damaturu, Satumba 25, 2024 (NAN) Rundunar ‘yan sandan jihar Yobe ta gargadi mazauna jihar da su yi taka-tsan-tsan da wasu mutane masu gayyatar tattaunawar karya a shafukkan zumunta na yanar gizo don gudin damfara.

DSP Dungus Abdulkarim, Kakakin rundunar ‘yan sandan ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Damaturu ranar Laraba.

Ya ce wata kungiya ce ta kikiri taron don yin anfani da shi wajen yaudaran jama’a da yi musu zamba cikin aminci.

“Masu satar bayanan jama’a sun kirkiri tarurrukan intanet na karya kuma suna aika sakonnin gayyata ta hanyar yanar gizo ga jama’a.

“Da zarar mutum ya danna hanyar haɗin yanar gizon, sai su yi masa kutse a asusun ajiyar sa na banki da sauran bayanan sirri,” in ji shi.

Kakakin ya ce a wasu lokutan, yan damfaran na fakewa da cewa su maikatan banki ne masu inganta asusun abokan cinikinsu.

” Sukan aika da lambar kalmar sirri ta OTP zuwa kafofin sada zumunta ko kuma wayar hannu, kuma su bukaceku da ku mayar da lambar sirrin don yin rijista ko kuma tabbatar da asusunku.

“Duk wanda ya yi haka, yana baiwa ‘yan damfarar damar cire kudi daga asusunsa cikin mintuna kadan,” in ji shi.

Jami’in ya kuma bukaci jama’a da su yi hattara da masu aikata laifuffukan yanar gizo tare da kaucewa bada bayyanan banki ga duk wanda bai cancanta ba.

Ya shawarci abokan huldar bankin da su tabbatar da irin wadannan bukatu ta hanyar kiran waya ko ziyartar bankunan su ko cibiyoyin hada-hadar kudi don karin bayan.

“Kada ka taɓa aika lambobin OTP ko mahimman bayanai zuwa wuraren da ba a tantance ba. Yi hattara da tarukan yanar gizo ko sabunta asusunka.

“Ku sa ido akan asusunku akai-akai kuma ku kai rahoton duk wani abun da ba daidai ba ga jamian tsaro,” in ji shi.

A cewarsa, kwamishinan ‘yan sandan jihar, Garba Ahmed, ya gargadi masu laifin da su daina aikata hakan ko kuma su fuskanci hukunci mai tsanani. (NAN) (www.nannews.ng)

NB/RSA

======

Rabiu Sani-Ali ya gyara

ICRC ta kwashe mutane 117 daga cibiyoyin kiwon lafiya 4 a Maiduguri

 

ICRC ta kwashe mutane 117 daga cibiyoyin kiwon lafiya 4 a Maiduguri

Ficewa

Daga Franca Ofili

Abuja, Satumba 23, 2024 (NAN) Kungiyar agaji ta Red Cross ta ce ta kwashe mutane 117 daga cibiyoyin kiwon lafiya hudu da ambaliyar ruwa ta shafa a jihar Borno.

Aliyu Dawobe, jami’in hulda da jama’a na ICRC ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa a ranar Litinin a Abuja.

Ya ce kungiyar ta kuma bayar da gudummawar jakankuna 150 ga hukumar NRCS, da asibitin kwararru na jihar da kuma hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar.

“ Madatsar ruwan Alau ta fashe ne da sanyin safiyar ranar 10 ga watan Satumba, abinda ya haddasa ambaliyar ruwa a Maiduguri.

“Kafin faruwar lamarin, ruwan sama kamar da bakin kwarya ya mamaye yankuna da dama a jihar lamarin da ya shafi hanyoyin shiga.

“Fiye da mutane 414,000 ne abin ya shafa tare da lalata gidaje da dama da amfanin gona.

“Akwai matukar damuwa ga fararan hula wadanda rikicin yankin ke cigaba da shafa,” in ji Dawobe.

A cewarsa, hadakar kungiyoyin agaji na ICRC da na NRCS ne ya shiga aikin bincike da ceton.

Ya ce sun kuma gudanar da aikin kwashe marasa lafiya tare da bayar da agajin gaggawa, da kuma hada kan iyalai da ambaliyar ruwa ta raba su da kuma kula da gawarwaki cikin aminci.

“Kungiyoyin sun kwaso gawarwaki 22 zuwa yau, yayin da yara 76 suka koma ga iyalansu.

“An kwashe mutane 117 daga cibiyoyin kiwon lafiya hudu da ruwan ya shafa.

“Hukumar ICRC ta kuma ba da gudummawar jakunkuna 150 ga NRCS, Asibitin Kwararru na Jiha da Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jiha (SEMA).

“NRCS ta kaddamar da ayyukan inganta tsafta a sansanoni uku da su ka karbi bakuncin al’ummomin da ambaliyar ruwa ta shafa tare da hadin gwiwar ICRC,” in ji Dawobe.

Dawobe ya ce a wani bangare na shirin rigakafin cutar kwalara, ICRC ta tanaji magunguna da suka hada AquaTabs da hodar chlorine don shirin ko ta kwana.

“Ana horar da masu aikin sa kai na NRCS kan yadda ake amfani da wadannan kayan kuma suna ba da fifiko wajen tsaftace rijiyoyi, famfunan hannu, rijiyoyin burtsatse, da sauran hanyoyin ruwa na al’umma.

“ICRC ta shirya zaman tallafi na zamantakewa don ma’aikatan NRCS da masu sa kai waɗanda suka shiga cikin ayyukan mayar da martani da yawa.

“A cikin kwanaki masu zuwa, ICRC tare da haɗin gwiwa tare da NRCS, za ta mika muhimman kayan gida ga gidajen da abin ya shafa, ciki har da taburmai, barguna, kayan dafa abinci, gidajen sauro, bokiti, sabulu, kayan tsaftacewa da tufafi, ” Yace.

A cewarsa, ICRC ta kuma taimaka wa Nijar, Kamaru da Chadi don magance matsalar ambaliyar ruwa.(NAN)( www.nannews.ng)

FNO/AMM

Fassara daga Nabilu Balarabe

=======

 

Gwamnatin Jihar Yobe ta sanarda yiwuwar sabuwar ambaliyar ruwa a kananan hukumomi 9

 

Gwamnatin Jihar Yobe ta sanarda yiwuwar sabuwar ambaliya ruwa a kananan hukumomi tara

Ambaliya

Daga Nabilu Balarabe
Damaturu, 11 ga Satumba, 2024 (NAN) Gwamnatin Jihar Yobe ta ce akwai yiwuwar samun sabuwar ambaliyar ruwa a kananan hukumomi tara na jihar a sakamakon shirin sakin ruwa daga madatsun ruwa na Dadinkowa da Lagdo.

Kananan hukumomin sun hada da Nguru, Bade, Karasuwa, Jakusko, Yusufari, Geidam, Tarmuwa, Bursari, Machina, Gujba da Fune.

Dokta Mohammed Goje, Babban Sakataren Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar (SEMA) ne ya yi wannan gargadin a wata sanarwa da ya fitar a Damaturu ranar Talata.

Ya kara da cewa sakin ruwa daga madatsun ruwan guda biyu zai kara jefa mazauna yankunan cikin mawuyacin hali.

” Mazaunan wadannan garuruwan sun sha wahala sosai saboda ambaliyar da ta auku a yankin a baya, sakamakon mamakon ruwan da aka kwashe kwanaki ana yi.

“Yobe ta fuskanci ambaliyar ruwa tsakanin 15 ga Afrilu zuwa 9 ga Satumba 2024, wanda ya haifar da barna a kananan hukumomi da dama.

“Wannan shawara ta kasance gargadi saboda yiwuwar fitowar ruwa daga dam ɗin Dadinkowa, Kogin Hadeja-Jama’are, Kogin Kamodugu, da kuma dam ɗin Lagdo a Kamaru,” in ji Goje.

Sakataren zartaswar ya shawarci mazauna yankunan da su dauki matakan kariya da suka hada da kauracewa zuwa wurin da babu alamun ambaliya domin ceton rayuka da dukiyoyin su.

“Ku kasance kuna da masaniya ta hanyar sauraron bayanai akai-akai daga shugabannin alumma, kananan hukumomi da hukumar ba da agajin gaggawa ta jiha.

“Ku ci gaba da tuntuɓar gaggawa wurin hukumomi don shirin kota-kwana,” in ji shi.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa sama da gidaje 19,000 a cikin al’ummomi 432 ne ya zuwa yanzu ambaliyar ruwa ta shafa a jihar. (NAN) (www.nannews.ng)
NB/KLM
======
Muhammad Lawal ne ya gyara

 

Ambaliyar ruwa ta kashe mutum 20, ta raba 2,000 da gidajensu a Yobe

 

Ambaliyar ruwa ta kashe mutum 20, ta raba 2,000 da gidajensu a Yobe

Ambaliyar
Daga Nabilu Balarabe
Gashua (Yobe), 7 ga Satumba, 2024 (NAN) Mutane 20 ne suka mutu sakamakon mummunar ambaliyar ruwa da ta afku a karamar hukumar Bade ta jihar Yobe tun farkon watan Agusta, in ji shugabanta, Alhaji Babagana Ibrahim.

Ibrahim ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Najeriya, (NAN) ranar Juma’a a Gashua cewa yawancin wadanda suka mutun sun makale ne a karkashin baraguzan gidajen laka da suka ruguje.

Ya ce ambaliyar ta lalata gidaje sama da 10,000 kuma ta yi awun gaba da filayen noma a cikin ya Kuna kusan 200.

Shugaban ya lissafa kauyukan da bala’in ya fi shafa da suka hada da Misilli, Lawan Musa, Dagona, Dala, Katuzu da Sabongarin Gashua.

Ya ce mutane 2,000 da ambaliyar ruwa ta raba da muhallansu suna samun mafaka a sansanoni uku  da a ka Taba da a Gashua.

Ya lissafa sansanonin a da suka hada da Goodluck, Zango 2 da Babuje.

Ibrahim ya ce majalisar karamar hukumar tana kokarin ciyar da ‘yan gudun hijirar abunci tun lokacin da suka zo sansanonin.

Ya ce kwanan nan Sanata Ahmed Lawan, tsohon shugaban majalisar dattawa ya bayar da gudummawar naira miliyan 10 ga wadanda abin ya shafa, yayin da gwamnatin jihar tuni ta fara raba kayan abinci ga wadanda abin ya shafa.

Ya kuma bukaci gwamnatin tarayya da ta kai dauki ga wadanda ambaliyar ruwa ta rutsa da su wadanda a kullum yawansu ke karuwa.

“ Mutane na cikin halin kaka-ni- kayi saboda girman wannan ibtila’in da ya faru kuma ya sha karfin karamar hukumar Bade.

“Don haka ne nake kira ga gwamnatin tarayya ta hannun Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA), da ta kawo mana agaji, ganin yadda ’yan gudun hijira ke ci gaba da karuwa,” in ji shi.(www.nannews.ng) (NAN)

NB/ETS

 

Gwamnatin Yobe ta bada gudummawar N30m ga iyalan mutanen da aka kashe a Mafa

Sallah janaizar mutanen da aka kashe a Mafa, Yobe

Gwamnatin Yobe ta bada gudummawar N30m ga iyalan mutanen da aka kashe a Mafa

Gudunmawa
Daga Nabilu Balarabe
Babangida (Yobe), 4 ga Satumba, 2024 (NAN) Gwamnatin Yobe a ranar Talata ta sanar da bayar da tallafin naira miliyan 30 ga iyalan wadanda harin ‘yantada masu tayar da kayar baya ya rutsa da su a Mafa a karamar hukumar Tarmuwa.

Wasu da a ke kyautata zaton mayakan Boko Haram ne sun kai hari garin Mafa a ranar Lahadin da ta gabata, inda suka kashe mazauna garin 34 tare da kona shaguna da gidaje a kauyen.

Mataimakin gwamnan jihar, Alhaji Idi Gubana ne ya bayyana hakan a lokacin da ya jagoranci wata tawaga zuwa Babbangida, hedikwatar Tarmuwa, domin jana’izar mutanen da aka kashe.

Ya jajanta wa Sarkin Jajere, Alhaji Mai Buba Mashio da al’ummar yankin bisa wannan aika-aikan.

Gubana ya umurci hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar (SEMA) da ta samar da matsuguni da kayan abinci ga ‘yan gudun hijirar da suka rasa dukkanin kayayyakinsu a sakamakon harin.

Ya bayyana cewa, Gwamna Mai Mala Buni, wanda ya nuna alhaininsa akan kashe-kashen, ya ziyarci babban hafsan tsaron kasa, Janar Christopher Musa, kan tabbatar da tsaro a Mafa.

Mataimakin gwamnan ya lura cewa tura isassun sojoji a Mafa – dake kan iyakar Borno da Yobe – zai hana kai hare-hare a cibiyar kasuwancin nan gaba.

Gubana ya yi addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasu ya kuma baiwa iyalansu hakurin jure rashin.

Da yake tsokaci game da harin, Birgediya-Janar Dahiru Abdulsalam mai ritaya, kuma mai ba da shawara na musamman kan harkokin tsaro na Gwamna Buni, ya karyata ikirarin cewa sama da mutane 34 ne suka mutu a harin.

” Adadin mutane 34 ne da aka samu gawarwakinsu, yayin da mutane 5 suka samu raunuka.

“Hudu na cikin mawuyacin hali, yayin da daya kuma ya samu rauni kuma yana cikin kwanciyar hankali.

” Duk wani bayani baya ga wannan jita-jita ce kawai. Ba wanda ya je Mafa jiya in ban da sojojin da suka kawo wadannan gawarwakin.

” ‘Yan tada kayar bayan ba sa fuskantar sojoji; suna fuskantar fararen hular da ba su ji ba ba su gani ba,” inji shi.(www.nannews.ng)(NAN)
NB/JI
Joe Idika ne ya gyara

 

Hamada na tilastawa mutane tserewa daga gidajensu a Jihar Yobe – Shugaban hukuma

Tapkin Tulo Tulo dake karamar hukumar Yusufari a jihar Yobe

 

Hamada na tilastawa mutane tserewa daga gidajensu a Jihar Yobe – Shugaban hukuma

Hamada
By Nabilu Balarabe
Damaturu, Augusta 30, 2024 (NAN) Kwararowar Hamada na cigaba da tilastawa al’umomi da dama a karamar hukumar Yusufari ta jihar Yobe barin yankunansu na asali.

Shugaban karamar hukumar, Alhaji Baba Aji, ya bayyana hakan ne a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) a Damaturu ranar Juma’a.

Ya ce dunkulewar yashi ya mamaye filaye da gidaje a cikin gundumominsu, lamarin da ya hana mutane da dabbobi da yawa cigaba da zama a yankunan.

“ Hamada ta kori mutane da yawa daga asalinsu. Wasu daga cikin wadannan mutanen yanzu haka suna samun mafaka a kauyen daban daban.

“Idan ka je kauyukan da abin ya shafa za ka ga dunkulewar yashi na ci gaba da matsowa kusa da gidaje.

“Wannan lamarin ya tilasta wa wasu daga cikinsu yin hijira zuwa garin Nguru.

“Sauran yankunan da hamadar ta shafa sun hada da Tulo-Tulo da Bula-tura, garuruwa biyu masu iyaka da Jamhuriyar Nijar.

“Garuruwanmu na fuskantar hadarin bacewa,” in ji Aji.

Shugaban ya bayyana damuwarsa kan cewa nan ba da jimawa hamadar za ta shiga wani tapki mai matukar muhimmanci wajen samar da ruwa a yankin, idan ba a dauki matakan gaggawa na dakile hakan ba.

“ Dunkulewar yashin na barazana ga wani tabki mai ban sha’awa wanda ya ke samar da ruwa don anfanin gida da shuke-shuke musamman lokacin rani

“Wannan haɗari ne a fili kuma ga tattalin arzikin jama’ar mu, ma su noman rake, tumatur, rogo, gyada har ma da dankali.

“Idan aka bar tafkin ya bushe, za a samu matsalar tattalin arziki don mutane za su rasa aikin yi,” in ji shi.

Aji ya bayyana cewa kokarin da karamar Hukumar, gwamnatin jinar, da aikin Great Green Wall na gwamnatin tarayya da ma kungiyoyi masu zaman kansu suka yi ya yi kyau, amma bai samar da sakamakon da ake bukata ba.

Don haka shugaban ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta samar da wani gandu a yankin domin dakile yashin.

“Ina kira ga ofishin asusun kula da muhalli da gwamnatin tarayya da su ayyana dokar ta-baci kan kwararowar hamada a karamar hukumar Yusufari.

“Muna buƙatar gagarimin shirin dashen itatuwa don hana cigaba da kwarrowar hamadar,” inji shugaban.

Akan shirin karfafa aikin gona na jihar, ya yabawa gwamna Mai Mala Buni, bisa yadda ya ware injinan gona da sauran kayayyakin amfanin gona wa yankin.

“Kayan aiki, taki da ingantattun iri da aka baiwa manoman sun zo akan gaba, lokacin da manoma suka fi bukata.

“ Saboda rarraba kayan gonan a kan kari, za mu girbi amfanin gona mai yawa a wannan shekara, Insha Allahu .

“Saidai mun fuskanci ambaliyar ruwa da zaizayar kasa a bana saboda ruwan sama kamar da bakin kwarya, lamarin da ya kai ga rugujewar gine-gine tare da lalata amfanin gonaki.

“Mun kai tawaga daga gwamnati da SEMA inda gine-ginen suka ruguje, kuma muna sa ran taimako daga gare su nan ba da jimawa ba.(www.nannews.ng)(NAN)
NB/YEN/HMH
============
Mark Longyen ne ya gyara
08032857987

Sojoji sun kama wani mutum bisa zargin karkatar da injinan gona a Yobe

 

Sojoji sun kama wani mutum bisa zargin karkatar da injinan gona a Yobe

Kame
Daga Nabilu Balarabe
Damaturu, Aug 27, 2024 (NAN) Dakarun Sojoji na Forward Operations Base (FOB) a Yobe sun kama wani mutum dan shekara 43 da haihuwa da injinan shuka guda 19.

Injinan na daga cikin kayayyakin gona da gwamnatin jihar ta rabawa manoma a baya-bayanan a karkashin shirinta na bunkasa noma.

Wannan na kunshe ne a wata sanarwa da Mai Bada Shawara Na Musamman ga Gwamna Mai Mala Buni, Brig.-Gen. Dahiru Abdulsalam maimurabus ya fitar.

Ya ce an kama mutumin ne da misalin karfe 12:10 na safiyar ranar Talata bayan ya boye injinan a cikin wata motar safa da ke kan hanyar Potiskum zuwa Gombe.

“Yau, da misalin karfe 00:10 na safe, sojojin FOB Potiskum sun kama wani mutum da injinan shuka iri 19.

“Kayan, wadanda ake zargin an fitar da su ne domin shirin karfafa ayyukan noma na jihar Yobe, an boye su ne a cikin wata motar bas mai dauke da kujeru 18 mai launin shudi mai lamba: KTG 449 YG,” in ji Abdulsalam.

Ya Kara da ce wanda ake zargin bai iya bayar da wata hujjar da ke nuna cewa shi ya ci gajiyar shirin ba.

“Maikayan ba shi da wata takadda da ke nuna cewar gwamnati ce ta bashi kayan ko ta ba wasu.

“Wanda ake zargin wanda ya fito daga Jigawa ya ce ya sayi kayan ne a hannun wani Alhaji Babaji mai lamba 08032837370 a Damaturu akan kudi N50,000.00 kowanne.

“Ya bayyana cewa zai kai kayayyakin Dutse a jihar Jigsawa don ya sayar,” inji shi.

Abdulsalam ya ce wanda ake zargin da kayayyakin da aka kwato za a mika su ga hukumar tsaro ta NSCDC domin gurfanar da su a gaban kuliya.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa Buni ya umarci jami’an tsaro da su kama duk wanda su ka samu yana kokarin fitar da injinan da ga jihar.(NAN) (www.nannews.ngg)
NB/SH
=====
Sadiya Hamza ta gyara

 

Gwamnatin Tarayya za ta tallafawa jihohin da ambaliyar ruwa ta shafa da N3bn

Gwamnatin Tarayya za ta tallafawa jihohin da ambaliyar ruwa ta shafa da N3bn

Tallafi
Daga  Muhammad Lawal
Birnin Kebbi, Agusta. 25, 2024 (NAN) Gwamnatin Tarayya ta ce za ta tallafa wa jihohin da ambaliyar ruwa ta shafa da Naira biliyan 3 domin dakile illolin da ke tattare da ibtila’in.

Mista Wale Edun, Ministan Kudi Da Gudanar da Tattalin Arziki ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a gidan gwamnati da ke Birnin Kebbi ranar Lahadi.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa ministan ya yi magana ne jim kadan bayan ya duba wasu yankunan da ambaliyar ruwa ta shafa a Kebbi.

Edun ya ce: “A nan zan sanar da cewa Majalisar Tattalin Arziki ta kasa ta himmatu kuma ta dauki matakin tallafa wa daukacin jihohin tarayya da kuma babban birnin tarayya Abuja da Naira biliyan 3 domin rage radadin ambaliyar ruwa a bana.

“Hakan zai sanya Jihohi da yawa kamar Kebbi cikin kyakkyawan yanayi don samun damar shirya manoman su don gudanar da duk wani muhimmin aikin noman rani, wanda muke tsammanin za a samu nasara, da tsare-tsare da kuma aiwatar da su yadda ya kamata.

Hakan a cewarsa, zai kai ga samun nasara, tare da samar da hanyoyin samar da abinci a farashi mai sauki da rage hauhawar farashin kayayyaki da kuma kara daidaita tattalin arzikin kasar.

Ya bayyana aniyar shugaban kasa Bola Tinubu na taimaka musu wajen tabbatar da tsaro, juriya da ingantawa da kara yawan amfanin da suke samu da kuma zama kwandon abinci a Najeriya.

Shima da yake jawabi, Ministan Tsare-tsaren Tattalin Arziki, Sen. Atiku Bagudu, ya koka kan yadda ambaliyar ta shafi kananan hukumomi da dama fiye da yadda ya gani a lokacin da ya ziyarci yankunan kwanan nan.

Sai dai ya yaba da juriya da kwarin gwiwa da mutanen Kebbi suke da shi, inda ya ba da tabbacin za a zaburar da su don yin aiki mai kyau a lokacin noman rani.

Ministan ya ce, baya ga Naira biliyan 3, gwamnatin tarayya ta amince da wani Asusun Renewed Hope Infrastructure Fund wanda za a yi amfani da shi wajen samar da hanyar Badagry zuwa Sokoto da wasu hanyoyin.

“Mafi tsawan doguwar hanyar zai kasance ne a yankin jihar Kebbi. Hakazalika, ban ruwa da madatsun ruwa muhimman fasalin wannan sabon asusun samar da ababen more rayuwan ne.

“Don haka, za a fadada wuraren noman rani a duk fadin titin mai kilomita 1,000 kuma wani muhimmin bangare na tallafin noman zai kasance a Kebbi,” in ji shi.

A nasa bangaren, Gwamna Nasir Idris, ya roki gwamnatin tarayya da ta taimaka wa jihar duba da yadda ambaliyar ruwa ta mamaye filayen noman shinkafa da dama a jihar.

Ya ce: “Sun je Wacot Rice Mill da ke Argungu kuma sun ga abubuwa da kansu. Sun kuma ziyarci Matan Fada a garin Argungu inda suka ga yadda ambaliyar ta shafi gonakin shinkafa.

“Kebbi ita ce kan gaba wajen noman shinkafa a kasar nan, saboda jihar noma ce.”
Gwamnan ya yi kira ga ministocin biyu da su tattauna da shugaban kasar kan yadda za a taimaki jihar Kebbi, inda ya ce jihar na da karfin ciyar da al’umma baki daya da ma sauran su.

A cewarsa, a kokarin da gwamnatin jihar ke yi na bunkasa samar da abinci a kasa, gwamnatin jihar ta raba takin zamani, da itatuwa, famfunan tuka-tuka, da injinan fanfo na CNG ga manoma sama da 35,000 kyauta.

Sai dai ya ce damina ta zo da kalubale da dama, tare da lalata filayen noma.

“Don haka muna son gwamnatin tarayya ta kawo mana agaji domin noman shinkafa ta gabato.

“Tuni mun fara wayar da kan manoman mu cewa nan da nan bayan girbin damina, gwamnati a shirye take ta taimaka musu su koma noman rani,” in ji shi.

NAN ta ruwaito cewa tawagar sun kuma ziyarci cibiyar kula da ruwa ta Dukku a Birnin Kebbi. (NAN)( www.nannews.ng )KLM/MNA
Maureen Atuonwu ta gyara
Nabilu Balarabe ya fassara