Sojojin Guinea-Bissau sun ayyana Janar a matsayin Shugaban sabon mulkin soja a kasar

Gabaɗaya

Dakar, 28 ga Nuwamba, 2025 (dpa/NAN) A ranar Alhamis ne sojojin kasar Guinea-Bissau da ke gabar tekun yammacin Afirka, suka sanar da nada sabon shugaba.

Gidan yada labarai na gwamnati TGB, ya ruwaito cewa Janar Horta Inta-A, zai yi aiki a matsayin shugaban rikon kwarya na tsawon shekara guda.

Ya zuwa yanzu dai, ba a fayyace komai game da daidaiton madafun iko a kasar da kuma yanayin da ake zargin juyin mulkin, kwanaki kadan bayan zaben shugaban kasar zai haifar ba.

Shaidun gani da ido sun shaidawa dpa cewa, titunan babban birnin kasar, Bissau, ba kowa, yayin da aka jibge sojoji a muhimman wurare a fadin birnin.

Kwana daya da ta gabata, wasu gungun jami’ai sun ce sun karbi mulki a kasar mai dauke da mutane kusan miliyan 2.2.

Sun ce sojoji sun bankado wani shiri na magudin zabe da kuma tada zaune tsaye a kasar, wanda ya hada da ‘yan siyasa da masu safarar miyagun kwayoyi.

Guinea-Bissau dai muhimmiyar cibiyar safarar hodar Iblis ce tsakanin Latin Amurka da Turai.

Rahotanni sun ce, shugaba Umaro Sissoco Embaló da aka hambare a yanzu, ya shaidawa kafar yada labaran Faransa cewa sojoji sun tsare shi. Sai dai ya ce ba a yi masa lahani ba.

An kuma ce sojoji sun tsare abokin hamayyar Embaló, Fernando Dias.

Duka Embaló da Dias, sun bayyana kansu a matsayin wadanda suka yi nasara bayan zaben shugaban kasar da aka gudanar a ranar Lahadi. Har yanzu ba a buga sakamakon zaben ba.

Kasar Guinea-Bissau dai ta fuskanci juyin mulki da yunkurin juyin mulki da dama tun bayan samun ‘yancin kai daga kasar Portugal a shekarar 1974.

Sojoji sun shafe shekaru da dama suna shiga siyasa sosai.

Tsohon Janar Embaló yana kan karagar mulki tun shekarar 2020, kuma ya rusa majalisar a karshen shekarar 2023.

A baya dai ya sha yin magana game da yunkurin juyin mulkin da aka yi masa, na baya bayan nan a watan Oktoba.

 

HS

===

Halima Sheji ta gyara

AAA/

Aisha Ahmed ta fassara

 

NELFUND za ta fadada lamuni zuwa ga dalibai masu horon sana’o’i

 

Lamuni

By Funmilayo Adeyemi

Abuja, Nuwamba 18, 2025 (NAN) Asusun bada lamunu na ilimin Najeriya (NELFUND), ya sanar da shirin tsawaita shirin ba da lamuni na dalibai don shirye shiryen koyon sana’o’i.

Manajan Darakta na NELFUND, Akintunde Sawyerr ne ya bayyana hakan a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) a Abuja.

Sawyerr ya ce tsarin fadadawar ya yi dai-dai da shirin gwamnatin tarayya na bunkasa ilimi da fasaha.

Ya kara da cewa matakin ya nuna yadda shugaban kasa Bola Tinubu, ya kuduri aniyar samar da ci gaban jarin masu sana’o’i fiye da ilimin jami’a na gargajiya.

“Babu wata al’umma da masana suka gina su kadai.

“Yana da matukar muhimmanci a sami mutanen da za su iya amfani da hannayensu, a kara masu kuzari, ƙarfafa su, da basira don aiwatar da dabaru masu wayo da ke fitowa daga waɗanda ke fitowa daga cibiyoyin ilimi,” in ji shi.

Sawyerr ya bayyana cewa, yayin da NELFUND ta fi mayar da hankali kan bayar da tallafin kudi ga dalibai a manyan makarantu tun lokacin da aka kaddamar da shi, aka fara shirye-shiryen fadada shi ga masu sana’a da fasaha a fadin kasar.

A cewarsa, mataki na gaba na ci gaban Najeriya yana bukatar daidaito tsakanin kwarewar ilimi da fasaha.

“A NELFUND, muna da hurumin yin sana’o’i.

“Ba mu fara ba tukuna, amma na san cewa gwamnatin shugaban kasa Bola Tinubu ta tabbatar da cewa an samu cikakken bayani kan batun.

” Ma’aikatar ci gaban matasa tana yin sana’o’i, ma’aikatar Ilimi ta shiga sana’o’i da kuma ma’aikatar tattalin arziki ta dijital ta shiga cikin dabarun IT.

“Don haka, fasaha wani abu ne da aka sa ma’aikatun gwamnati da yawa da aikatawa.

“Kuma ina ganin a fili yake cewa injiniyan da zai iya yin gini, ya fi injiniyan da zai iya zane kawai.

“Matakin da muke a kasar nan a yanzu, shine abin da zan kira, tsarawa, ginawa, da sarrafa matakin,” in ji shi.

(NAN)( www.nannews.ng )

FAK/ROT

=======

Rotimi Ijikanmi ne ya gyara shi

Aisha Ahmed ta fassara shi.

Nnamdi Kanu ya kori kungiyar lauyoyi masu kare shi, ya kalubalanci hurumin kotu

 

By Taiye Agbaje

Abuja, Oktoba 23, 2025 (NAN) Nnamdi Kanu, shugaban masu fafutukar kafa kasar Biafra (IPOB), a ranar Alhamis, ya bayyana korar tawagar lauyoyinsa, karkashin jagorancin Cif Kanu Again, SAN, a babbar kotun tarayya dake Abuja.

Kanu, ya shaida wa mai shari’a James Omotosho, a zaman da aka ci gaba da zaman, cewa a shirye yake ya kare kansa.

Biyo bayan matakin da shugaban kungiyar ta IPOB ya dauka, dukkan manyan masu fafutuka a cikin kungiyar da suka hada da Cif Agabi, tsohon babban lauyan gwamnatin tarayya (AGF), sun janye daga ci gaba da fitowarsu a shari’ar.

Dangane da wannan al’amari, Kanu, wanda a yake gabatar da jawabi a gaban kotun, ya kalubalanci hurumin kotun da ta gurfanar da shi.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN), ya ruwaito cewa Kanu ya sanya hannu a kan korafinsa kuma ya shigar da shi a ranar 21 ga watan Oktoba.

Ya kuma sanya tsohon babban lauyan gwamnatin tarayya, Abubakar Malami da sauran su, a matsayin shaidu a ci gaba da shari’ar da ake yi na zargin ta’addanci, kuma ya jera manyan mutane da dama a matsayin shaidu.

Daga cikin wadanda Kanu ya lissafa a matsayin “shaidu masu karfi” akwai Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike; tsohon ministan tsaro, Janar Theophilus Danjuma mai ritaya da kuma tsohon babban hafsan sojin kasa, Janar Tukur Buratai mai ritaya.

Sauran sun hada da, Gwamna Babajide Sanwo-Olu na jihar Legas, Gwamna Hope Uzodinma na Imo, ministan ayyuka, Dave Umahi, tsohon Gwamnan Abia, Okezie Ikpeazu, da tsohon Darakta-Janar, Hukumar Leken Asiri ta (NIA), Ahmed Abubakar.

Sauran sun hada da tsohon shugaban hukumar tsaro ta farin kaya, Yusuf Bichi, da kuma shaidu da dama da bai bayyana sunayensu ba.

Kanu, a cikin karar, ya yi alkawarin gabatar da bayanan rantsuwar dukkan shaidun, na son rai ga wannan kotu mai girma, kuma za su sanar da masu gabatar da kara a lokacin da ya  dace.

Hakazalika, NAN ta ruwaito cewa shugaban na IPOB ya yi ganawar sirri da tawagar lauyoyin sa a babbar kotun kasa a Abuja ranar Laraba.

Kanu wanda jami’an hukumar tsaro na farin kaya (DSS) suka gabatar da shi a kotu, ya gana da ‘yan kungiyar llauyoyin nasa a kotun mai shari’a James Omotosho, kamar yadda aka umarta a baya.(NAN)(www.nannews.ng)

TOA/SH

Fassarar Aisha Ahmed 

=====

 

Shugabar wata karamar hukuma a Legas ta haramta cinikin gefen hanya

Gefen hanya

Daga Idris Olukoya

Epe (Lagos), Oktoba 23, 2025 (NAN) Shugabar karamar hukumar Epe ta jihar Legas, Ms. Surah Animashahun, ta yi gargadi da a daina yin ciniki a gefen titi a yankin, saboda hadurran da ke tattare hakan da kuma cunkoson ababen hawa.

Animashahun, ta shaidawa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a ranar Alhamis cewa, matakin ya zama dole domin inganta zirga-zirgar ababen hawa, da inganta lafiyar jama’a, da kuma maido da tsari a wuraren da jama’a ke cunkoso.

Ta ce, an kai samame ne a kan muhimman wurare kamar; Kasuwar Aiyetoro, Tsohon Garage Ijebu-Ode, Ita-Opo, Kasuwar Inuwa da sauran wuraren da aka gano a cikin al’umma.

“Yan kasuwa a wadannan yankuna sun samu koma bayan tsarin hanya da kuma hanyoyin tafiya, domin hakan  na haifar da hadari mai tsanani.

“Daga yanzu, majalisar ba za ta amince da yin cinikin gefen hanya ba, saboda hadurra da cunkoson ababen hawa,” in ji ta.

Shugaban ya ce jami’an kungiyar yaki da rashin da’a ta Kick Against Indiscipline (KAI), za su zagaya domin gudanar da ayyukan dakile cin hanci da rashawa da ake yi a kan tituna a fadin al’umma.

Animashahun, ta kuma bayyana cewa, an samu hadurra da dama a kan titin Aiyetoro, wanda ya yi sanadin asarar rayuka da dukiyoyi sakamakon tukin ganganci.

“Ba za mu iya ci gaba da jure asarar rayuka da dukiyoyi ba sakamakon rashin da’a daga mutanenmu, saboda hanyoyin mota ne, ba na kasuwanci ba,” in ji ta.

Ta bayyana cewa, karamar hukumar ta samar da wurin da ya dace a bayan kasuwar Aiyetoro domin ‘yan kasuwa su gudanar da harkokinsu lafiya ba tare da hana zirga-zirga ba.

“Mun yi isassun shirye-shirye domin ‘yan kasuwarmu su yi cinikinsu a bayan kasuwa, inda masu ababen hawa ba sa wucewa, a hukumance an kebe wurin domin yin ciniki,” inji ta.

Shugaban karamar hukumar, ta bada tabbacin cewa ana ci gaba da kokarin sake gina kasuwar Aiyetoro, wadda ta ruguje a zamanin gwamnatin tsohon gwamna Akinwunmi Ambode.

Ta kara da cewa, nan ba da dadewa ba, za a sake gina kasuwar a karkashin jagorancin Gwamna Babajide Sanwo-Olu, inda ta cigaba da cewa, tattaunawa da tsare-tsare sun yi nisa.

NAN ta ruwaito cewa, ‘yan kasuwa a wuraren da abin ya shafa kamar, Aiyetoro, Ita-Opo, Shade, Popo Oba, da Papa, an umurce su da su koma kasuwannin da gwamnati ta amince da su.

Karamar hukumar ta kara yi gargadin cewa, duk dan kasuwan da ya karya dokar zai fuskanci takunkumi a atisayen aiwatar dokar a gaba.

Animashahun ta cigaba da cewa ba wai an yi wannan shiri ne don farautar kowa ba, sai don tabbatar da tsari, da’a da kuma tsaron mazauna yankin.

Ta yi kira ga shugabannin kasuwar, da shugabannin al’umma da su wayar da kan ‘ya’yansu akan muhimmancin bin doka da oda, inda ta jaddada cewa gyare-gyaren harkokin gudanar da birane za su ci gaba da samun fifiko a karkashin gwamnatinta. (NAN)(www.nannews.ng).

 

SIO/KOLE/CHOM

========

 

Remi Koleoso/Chioma Ugboma ne ya gyara shi

Aisha Ahmed ta fassara

Wata gidauniya ta zaburar da sarakuna domin yaki da cin zarafin mata a Bauchi

Daga Amina Ahmed

Ningi (Bauchi srate), Oktoba 23, 2025 (NAN) Wata kungiya mai zaman kanta, Ikra Foundation for Women and Youth Development (IKFWYD), ta fara wani shiri na shekaru biyu, don zaburar da maza wajen magance cin zarafi.(GBV).

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya ya ruwaito cewa ana aiwatar da shirin ne a kananan hukumomin Bauchi, Ningi, da Toro.

Jami’in sa ido da tantancewa na gidauniyar, Isma’il Umar ne ya bayyana hakan a wani taron bayar da shawarwari da aka gudanar da hakiman kananan hukumomi a garin Ningi.

Ya ce rawar da cibiyoyin gargajiya ke takawa na yin tasiri mai kyau wajen canza halayya tare da hana wuce gona da iri ba.

“An tsara shirin ne domin jawo hankalin maza, kan batutuwan da suka shafi kare hakkin mata da ‘ya’ya mata baki daya.

“Ba za a iya samun jin daɗin iyali da haɗin kai ba, ba tare da sa hannun maza ba,” in ji shi.

Umar ya lura cewa, kalubale kamar rashin fahimtar juna ta jinsi, rashin fahimtar juna a cikin gida, rashin fahimtar juna a tsakanin ma’aurata, da karancin sanin nauyin da ya rataya a wuyansu na haifar da rashin zaman lafiya a iyali.

“In aka mayar da hankali ga maza a matsayin abokan haɗin gwiwa don inganta zaman lafiya da walwala, wannan shirin yana da nufin ƙarfafa tasirin su a cikin iyalai da al’ummomi,” in ji shi.

Umar ya kara da cewa, shirin zai samar da hadin kai tsakanin maza da mata, wajen wanzar da zaman lafiya a gidajen aure.

Shi ma da yake jawabi, Mista Bamidele Jacobs, Daraktan Shari’a na Lauyoyin Alert, ya ce Lauyoyin ALert da Iqra Foundation, za su aiwatar da shirin na tsawon shekaru biyu.

A cewarsa, maza na da matukar muhimmanci wajen dakile barazanar GBV, ya kara da cewa za a zabi zakarun maza don gudanar da shirin.

A nasu jawabai mabambanta, sarakunan gargajiya sun bayyana goyon bayansu da jajircewarsu ga shirin.

Hakimin Ningi, Alhaji Yusuf Danyaya, ya yi alkawarin zaburar da maza domin gudanar da wannan shiri, inda ya ce “gidan da babu tashin hankali yana haifar da zaman lafiya a cikin al’umma.”

Hakazalika, Hakimin Miri da ke cikin birnin Bauchi, Alhaji Hussaini Uthman, ya ce manufar shirin ta yi daidai da irin rawar da shugabannin al’umma ke takawa wajen samar da sulhu a tsakanin ma’aurata.

A nasa bangaren, Hakimin Toro, Alhaji Umar Adamu, ya ce, yin jawabi akan GBV, wani nauyi ne da ya rataya a wuyansu domin tabbatar da cewa al’umma sun kasance cikin aminci da lumana. (NAN) (www.nannews.ng)

 

AE/BEKl/KLM

iEdited by Abdulfatai Beki/Muhammad Lawal

Fassarar Aisha Ahmed 

 

Gwamnatin Tarayya ta jajantawa Gwamna Bago, al’ummar Nijar bisa fashewar tankar mai

Ta’aziyya

By Collins Yakubu-Hammer

Abuja, Oktoba 23, 2025 (NAN) Gwamnatin tarayya ta jajanta wa gwamnati da al’ummar Neja bisa fashewar wata tankar man fetur a garin Essa, da ke karamar hukumar Katcha a jihar.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na kasa, Alhaji Mohammed Idris, ya fitar ranar Alhamis a Abuja

Takardar ta bayyana matukar alhininsa bisa afkuwar lamarin da yayi sanadin salwantar rayuka da kuma jikkata wasu da dama.

“Muna tare da gwamnati da al’ummar jihar Neja wajen jimamin wannan rashi.

“Wannan lamari mai ratsa zuciya, ya sake haifar da mummunar illar hadurran tankar mai a cikin al’ummarmu.

“Gwamnatin tarayya, ta yi bakin cikin cewa, duk da cigaba da wayar da kan jama’a tare da gargadi game da illolin kwasar man fetur daga fadowar tankunan man fetur, har yanzu wasu na yin kasadar da ke barazana ga rayuwa.

“Kowane ran dan Najeriya yana da daraja, kuma irin wadannan bala’o’in za a iya kauce musu sun zama izina domin ƙarin kulawa da bin umarnin tsaro,” in ji Idris.

Ya yaba da yadda gwamnatin Neja, hukumomin tsaro da masu bada agajin gaggawa, suka gaggauta daukar matakin kashe gobarar, tare da ceto wadanda suka tsira da rayukansu, kuma suka bayar da tallafi ga iyalan wadanda abin ya shafa.

Ministan ya ce an kuma umurci Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa (NEMA), da ta kara kaimi akan kokarin da gwamnatin jihar ke yi na samar da agaji da magunguna ga wadanda abin ya shafa da iyalansu.

“Gwamnatin tarayyar ta kuma umurci hukumar wayar da kan jama’a ta kasa, da ta kara kaimi wajen wayar da kan jama’a a fadin kasar.

“A kara tsaurara matakan tsaro, musamman a yankunan karkara da masu fama hadariurra, domin hana sake afkuwar irin wannan bala’i.

“Tunaninmu da addu’o’inmu suna tare da wadanda abin ya shafa tare da iyalansu, da daukacin al’ummar Neja a wannan lokaci na bakin ciki.

“Allah Ya jikan wadanda suka rasu, kuma Allah Ya bawa ‘yan’uwansu ikon jure wannan rashi mai raɗaɗi,” in ji Idris. (NAN) (www.nannews.ng)

 

CMY/BEKl/BRM

==============

Edited by Abdulfatai Beki/Bashir Rabe Mani

Fassarar Aisha Ahmed

 

Wata mata ta nemi kotu ta raba aurenta saboda rashin soyayya

Soyayya

By: Mujidat Oyewole

Ilorin, Oct. 23, 2025 (NAN) Wata mata mai suna Misis Hajara Busari, ta roki wata kotu da ke garin Ilorin, da ta raba aurenta da mijinta, Mista Mumini Anafi, shekaru shida da suka gabata, saboda rashin soyayya.

Mai shigar da kara ta shaida wa kotun a ranar Alhamis cewa, ita ba ta da sha’awar auren na bisa addinin Musulunci da mijinta, kuma ta bukaci kotun da ta raba su.

Tace tana neman umarnin a raba aure, kuma a bata hakkin kula da ‘ya’yanta uku, da kuma kudi N50,000, a matsayin kudin kula da ‘ya’yanta.

A halin da ake ciki, mijin da ake kara, ya shaida wa kotun cewa har yanzu yana sha’awar zaman aure da matarsa, kuma ya bukaci kotun da kada ta yi sassauci akan abunda mai shigar da kara ya nema.

Alkalin kotun, Mista Toyin Aluko, ya bukaci maigidan da ya binciko duk wata dama da zai samu, domin samun sulhu cikin lumana kan duk wata takaddama da matarsa.

Kotun ta dage ci gaba da sauraron karar har zuwa ranar 17 ga watan Disamba, domin samun rahoton sasantawa ko kuma sauraron karar. (NAN)www.nannews.ng

 

MOB/UNS

======

 

Sandra Umeh ta gyara

Aisha Ahmed ta Fassara

Hukumar NESREA ta lalata buuhunan sassan jikin jakuna 700 da Kwastam ta mika mata

Jaki

Doris Esa

Abuja, Oktoba 16, 2025 (NAN) Hukumar Kula da Muhalli ta Kasa (NESREA) ta ce, ta lalata buhunan sassan jikin jakuna 700 da Hukumar Kwastam ta Najeriya ta mika mata a Kaduna.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Misis Nwamaka Ejiofor, mataimakiyar daraktar yada labarai ta NESREA ta fitar a Abuja.

Ta ce hakan ya yi daidai da ka’idojin muhalli da ka’idojin aminci.

Ejiofor ta ce, an lalata kasusuwan jakuna da fatun ne a ranar 3, 4 da 6ga watan Oktoba, a Kaduna.

“An yi amfani da wurare guda biyu don kona kasusuwan, yayin da aka binne fatun a wani wuri da aka kebe.

 “An gudanar da atisayen ne a gaban jami’an tsaro kuma bisa ka’idojin muhalli,” in ji shi.

Ta ce an samu nasarar gudanar da atisayen ne ta hanyar hadin gwiwar hukumar ta NESREA da hukumar Kwatam.

Ejiofor ta kara da cewa, sun tabbatar da cewa an yi aikin ne cikin aminci da kiyaye muhalli.

“Wannan ya nuna gagarumar nasara, a kokarin da ake na yaki da fataucin namun daji da kuma kare nau’o’in su da ke cikin hadari.

 “An gudanar da aikin ne a ƙarƙashin tsauraran ka’idojin hadin gwuiwa, don hana duk wani haɗarin muhalli ko lafiya.

“Ma’aikatun da ke cikin atisayen sun sanya kayan kariya na sirri, kuma an dauki matakan rage hadarin kamuwa da duk wata illar da za ta shafi rayuka,” in ji ta.

Ejiofor ta jaddada cewa hukumar NESREA a watan Yuli ta kona sama da buhu dari na al’aurar jakuna da hukumar kwastam ta Najeriya ta mika a Abuja.

Darakta Janar na Hukumar NESREA, Farfesa Innocent Barikor, ya koka da yadda jakuna ke raguwa a Najeriya, ya yi gargadin cewa sannu a hankali suna mutuwa.

Barikor ya jaddada tsayuwar daka da gwamnatin Najeriya ta ke yi na yaki da safarar jakuna ba bisa ka’ida ba.

Ya ce an dauki jakuna dabbobin gida, amma bukatarsu da masu safarar miyagun kwayoyi suke yi don yin maganin kara karfin sha’awa, ya sa gwamnatin tarayya ta ba da umarnin hana sayar da ita.

Barikor ya ce, lalata sassan jakunan da hukumar NESREA da NCS suka yi, an yi shi ne don hana fataucin jakunan ba bisa kaida ba.

Ya yi godiya ga hukumar ta Kwastam bisa gagarumin goyon baya ga yaki da fataucin miyagun kwayoyi da ke cikin hadari. (NAN) (www.nannews.ng)

 

Chidi Opara ya gyara ORD/CEO

Aisha Ahmed Ta fassara.

Gwamnatin jihar Jigawa ta amince da karin kasafin N75bn

 

Kasafin kudi

by Aisha Ahmed 

Dutse, Sept.18, 2025 (NAN) Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da karin kasafin kudi na Naira biliyan 75, na kasafin kudi na shekarar 2025, domin mikawa majalisar dokokin jihar gaba daya.

Kwamishinan Yada Labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu, Mista Sagir Musa ne ya bayyana haka, a wata hira da aka yi da shi ranar Laraba a Dutse, jim kadan bayan kammala taron majalisar zartarwa ta jiha. 

Ya ce rabon kasafin ya taso ne saboda karin kudaden shiga da aka samu.

“Dalilin kara kasafin kudin shine don magance bukatun kudi da suka kunno kai da kuma karfafa bangarorin da muka sa a gaba domin samun ci gaba mai dorewa a fadin jihar. 

“Alkaluman da aka amince da su sun kai biliyan ₦58 na Gwamnatin Jiha, da kuma Naira biliyan 17 na kananan hukumomi 27, wanda ya hada da na yau da kullum da kuma manyan kudade,” inji shi.

Ƙarin kasafin, in ji shi, zai haɓaka ayyuka da shirye-shirye masu gudana a sassa masu mahimmanci kamar ilimi, kiwon lafiya, kayayyakin more rayuwa, aikin gona, da sauran  ayyukan ci gaba.

Ya ce hakan zai kuma bayar da tallafin kasafin kudi don sabbin bukatu na kashe kudi da ba a zata ba, tare da daidaita kashe kudaden jama’a tare da tattalin arziki da kuma manufofin ci gaba.

Kwamishinan ya ce, za a mika kudurin karin kasafin kudin ga majalisar dokokin jihar ta Jigawa, domin tantancewa tare da amincewa da shi, kamar yadda tsarin mulki ya tanada. 

Musa ya ce, matakin ya nuna yadda gwamnati ta himmatu wajen tabbatar da gudanar da mulki cikin gaskiya, kula da harkokin kudi da kuma samar da ingantaccen hidima ga daukacin al’ummar Jigawa.

NAN ta ruwaito cewa, Gwamna Umar Namadi ya sanya hannu kan kasafin kudin jihar na shekarar 2025 na Naira biliyan 698.3 a ranar 1 ga watan Janairu, wanda ya kasance  mafi girma a tarihin jihar.

A nasa jawabin, Namadi ya bayyana kasafin a matsayin mai kawo sauyi da kuma muhimmanci ga ci gaban jihar cikin dogon lokaci.

“Kasafin kudin bana na Naira biliyan 698.3 shi ne mafi girma a tarihin jihar Jigawa, an tsara shi ne domin sake fasalin jihar zuwa mafi girma,” inji shi.

Kashi 76 cikin 100 na kasafin kudin an ware su ne ga manyan ayyuka, wanda hakan ya nuna muhimmancin gwamnatin kan samar da ababen more rayuwa da ci gaba.

Namadi ya bayyana cewa, wadannan jarin za su kafa tushen ci gaban tattalin arziki mai dorewa da kuma inganta rayuwar al’umma a fadin jihar.  (NAN) (www.nannews.ng)

 

AAA/SH

Rahoto da fassarar Aisha Ahmed

Najeriya na asarar dala biliyan 10 a duk shekara sakamakon asarar bayan girbi – Kyari  

 

Bayan girbi

Daga Aisha Ahmed 

07030065142

Kangire, (Jigawa), Satumba 16, 2025 (NAN) Ministan Noma da Samar da Abinci, Sen. Abubakar Kyari, ya ce Najeriya na asarar dala biliyan 10 a duk shekara sakamakon asarar da ake yi bayan girbi.

Kyari ya bayyana haka ne a yayin bikin kaddamar da kungiyar noma da samar da ababen more rayuwa a karkara (GRAIN) Pulse Center a kauyen Kangire, na karamar hukumar Birnin-Kudu, Jigawa.

Ya ce ana tafka asara ne sakamakon rashin wajen ajiya, rashin ababen more rayuwa, karancin kayan sarrafawa, dumamar yanayi, ambaliyar ruwa, gurbacewar kasa, da karuwar ruwan sama a fadin kasar.

A cewarsa, noma na bayar da kusan kashi 24 cikin 100 na GDPn Najeriya, inda kananan manoma ke noma kusan kashi 70 cikin 100 na abincin kasar.

“Ta hanyar karfafa wa kananan manoma da kayan aiki na zamani, fasaha, da kasuwanni, za mu iya zakulo cikakkiyar arzikin ƙasarmu da mutanenmu,” in ji Ministan.

 Kyari ya jaddada kudirin gwamnatin shugaba Bola Tinubu, na baiwa harkar noma fifiko a matsayin ginshikin kawo sauyi ga al’ummar kasar, yana mai jaddada cewa an mayar da hangen nesa zuwa aikace.

Ya bayyana yadda tsare-tsaren kamfanoni masu zaman kansu ke da muhimmancin gaske wajen karfafa tsarin abinci a Najeriya da kuma karfafa juriya kan asarar da ake yi bayan girbi.

Ministan ya ce, cibiyar pulse zata yi aiki ne a matsayin hadaddiyar cibiyar noma, samar da ababen more rayuwa, da raya karkara, ta yadda za ta hada dukkan sassan aikin gona waje guda.

Ya kara da cewa, cibiyar da aka tanadar na da kayan aiki na zamani, za ta samar da yanayi mai aminci na fitar da kayayyaki zuwa kasashen ketare, kuma za a yi irin ta a fadin kasar baki daya.

Har ila yau, Ministan Harkokin Waje, Amb. Yusuf Tuggar, ya jaddada karfin hadin gwiwar gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu, wajen ci gaba.

Ya kuma yaba da yadda aka samar da irin wadannan cibiyoyi a cikin al’ummomin noma na Jigawa.

“Wannan yunkuri zai amfanar da Najeriya saboda fa’idodi da yawa, musamman haɗa kayan aiki da fasaha na zamani,” in ji Tuggar.

Ya yabawa shugaba Tinubu da gwamnan Jigawa ta Umar Namadi, kan yadda suka ba da fifiko wajen samar da abinci a cikin manufofin ci gaban su.

Gwamna Namadi ya bayyana jin dadinsa da yadda Jigawa ta karbi bakuncin cibiyar na farko a kasar, inda ya bayyana ta a matsayin wata kyakkyawar fasaha domin dorewar rayuwar karkara.

Ya ce aikin zai zaburar da tattalin arziki, tare da nuna sauye-sauyen da al’umma za su samu ta hanyar bunkasa noma.

Namadi ya bayyana cewa, wurin ya hada da tsarin hadaka mai amfani da hasken rana, cibiyoyin sadarwa na zamani, da kuma hidimomin da suka kunshi dukkan sassan darajar aikin gona.

Ya nanata kudirin gwamnatinsa na karfafa aikin gona domin samar da ayyukan yi, fadada ababen more rayuwa, da inganta rayuwa.

Shugaban Karamar Hukumar Birnin-Kudu, Mista Muhammad Uba, ya yi alkawarin ba da goyon baya ga ajandar Shugaba Tinubu, inda ya bayyana yadda jihar Jigawa ta ba da fifiko a fannin noma da samar da abinci.

Ya kara da cewa Gwamna Namadi ya dauki muhimman matakai domin kawo sauyi da kuma daidaita harkar noma a jihar.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa Kyari ya kaddamar da cibiyar GRAIN Pulse Centre a Kangire, a wani bangare na shirin sabunta bege. (NAN) (www.nannews.ng)

AAA/KTO

 

======

Fassarar Aisha Ahmed