Ambaliyar ruwa ta lalata gidaje, gonaki 80 a Langtang ta Kudu
Ambaliyar ruwa ta lalata gidaje, gonaki 80 a Langtang ta Kudu
Ambaliyar ruwa
By Polycarp Auta
Jos, Oktoba 6, 2024 (NAN) Wata mummunar ambaliyar ruwa da ta afku a karamar hukumar Langtang ta Kudu a jihar Filato, ta lalata gidaje da gonaki 80.
Ambaliyar wadda ta afku a tsakanin Juma’a da Lahadi, ta raba dubban mutane da muhallansu tare da yin awun gaba da kayayyakinsu.
Saidai an yi sa’a, ba ta yi asarar rayuka ba.
Mista Yintim Nimilam, sakataren kungiyar ci gaban al’ummar Sabon Gida, ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici, inda ya bayyana yadda sama da iyalai 80 suka rasa matsugunnansu.
“Yan gudun hijirar suna neman mafaka a gurin makwabta, abokai, da dangi,” ya ce.
Wani mazaunin garin, Mista Nandul Solomon, ya bayyana damuwar al’ummar, inda ya yi kira da gwamnati da ta dauki matakin gaggawa domin rage musu radadi.
“Muna kira ga gwamnati da hukumomin da abin ya shafa da su kawo mana dauki.” (NAN) ( www.nannews.ng )
AZA/AMM
Abiemwense Moru ne ya gyara
Fassara daga Nabilu Balarabe